Isa ga babban shafi
Turkiya

"Turkiya ba za tura dakaru zuwa Syria ba"

Firaministan Turkiya Ahmet Dovutoglu ya yi watsi da matakin tura dakaru zuwa yankin da kasar ke yi wa mayakan Jihadi ruwan wuta a Syria ba, kamar yadda ya tabbatar wa manema labarai a yau Litinin.

Firaministan Turkiya Ahmet Davutoglu
Firaministan Turkiya Ahmet Davutoglu REUTERS/Umit Bektas
Talla

Wannan na zuwa ne bayan Turkiya ta kaddamar da hare haren sama kan mayakan Kurdawa a arewacin Iraqi da kuma mayakan ISIL da ke da’awar jihadi a Syria.

Davotoglu ya ce za su ci gaba da kai wa IS da PKK hare hare ta sama a Iraqi da Syria ba tare da aikawa da dakarun kasa ba.

Turkiya na zargin kungiyar kurdawa ta PKK da kai wani harin bam wanda ya kashe sojojin kasar biyu, a kudu maso gabashin kasar inda kurdawa suka fi yawa, zargin da ke zuwa a dai-dai lokacin da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu ke tangal-tangal.

A dai cikin makon da ya gabata ne aka danawa motar da sojojin Turkiya ke ciki bam a lardin Lice, wanda da ya yi ajalin sojoji biyu tare da jikata wasu hudu.

Kuma Zargin Turkiya ya biyo bayan kona wasu ababben hawa da ‘yan tawayen kungiyar kurdawa na PKK suka yi a inda aka kashe dakarun Turkiya

Turkiya dai ta kaddamar da hare-haren sama mai tsanani da na artilare kan Mayakan Jihadin ISIL da kuma kurdawa, saboda barazanar tsaro da ta ke fuskanta.

Matakin da a yanzu ya sabawa yarjejeniyar zaman lafiya da kasar ta cim ma da kungiyar PKK ta kurdawa a cikin shekarar ta 2013.

Kungiyar PKK ta ce karya dokokin zaman lafiya da Turkiya ta yi bayan kai hare-hare kan kurdawan Iraqi zai kara dawo da sabanin da ke tsakaninsu.

Yanzu haka Kasashen kungiyar tsaro ta NATO na shirin gudanar da taro a ranar Talata domin tattaunawa halin da ake ciki a kasar Turkiyya, sakamakon hare-haren da kasar ta kaddamar akan mayakan ISIS da kuma kungiyar Kurudawa ta PKK.

Sanarwar NATO na cewa Turkiya ce ta bukaci a gudanar da wannan taro na gobe a birnin Bruxelles na kasar Belguim.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.