Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa ta yi watsi da salon tattaunawar Iran

Koriya ta Arewa ta ce kasashen duniya su dai na tunanin za a samu yin tattaunawa tsakaninta da Amurka domin samun nasarar irin sulhun da aka cim ma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan shirin Nukiliya.

Kim Jong-un Shugaban Koriya ta Arewa
Kim Jong-un Shugaban Koriya ta Arewa REUTERS/KCNA
Talla

Koriya ta Arewa ta jaddada mallakar makamin Nukiliya wanda ya sha banban da na Iran.

Kuma Koriya ta yi watsi da duk wani mataki na shiga sulhu da ita, wannan kuma na zuwa ne duka mako guda bayan manyan kasashen duniya sun yi nasarar cim ma yarjejeniya da Iran.

A wata sanarwar da ta fitar a safiyar Talata, ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta ce zai kasance abu mai wuya a iya samun kusantar juna tsakanin kasar da Amurka kan shirin nukilyarta.

Sanarwar ta ce shirin Nukiliyar Koriya tun da farko ya yi hannun riga da salon siyasa kasar Amurka, saboda haka ba ta yadda za a kwatanta shirin nukiliyar kasar da kuma na Iran.

Ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta ce lura da salon a tsokana da Amurka ke amfani da shi da suka hada tsaurara takunkumai da kuma shirye atisayen soji a kasashe masu makwabtaka da ita, wasu alamu ne da ke tabbatar da cewa Amurka ba ta bukatar zaman lafiya ko samun sulhu.

Gwamnatin ta Koriya ta ce babu wani alfanu ga shiga tattaunawa da nufin hana wani samun damar mallakar wata baiwa ko fasahar da Allah ya ba wata kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.