Isa ga babban shafi
Amurka

Shahararren Mawakin Amurka 50 cent ya fada a kwata

Shahararren Mawakin kasar Amurka da ake kira Curtis James Jackson ko kuma 50 Cent ya ce halin da ya samu kan sa a cikin yanzu bashi da kumbar susa bayan alkali ya umurce shi ya biya wata mata dala miliyan 5 saboda daukar ta a hoton da ya yi babu kaya a jikin ta wanda akayi ta wallafa shi a intanet.

Shaharren mawaki 50 cent
Shaharren mawaki 50 cent Wikimedia/photosbyalyssa
Talla

Mujallar Forbes da ke wallafa attajiran duniya ta ce 50 Cent ya mallaki dala miliyan 150 bana, sakamakon jarin sa da ya sayar a wani kanfani inda ya karbi kudin da suka kai dala miliyan 100.

Sai dai takardun da ya shigar kotu dan kare shi daga biyan basusukan da ake bin sa sun nuna cewar yanzu kadarorin 50 Cent basu wuce Dala miliyan 10 ba yayin da bashin da ake bin sa suka zarce Dala miliyan 50.

Shi dai mawakin mai shekaru 40 an haife shi ne cikin talauci, inda aka kashe mahaifiyar  wadda ke safarar miyagun kwayoyi a birnin New York lokacin yana karami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.