Makomar tattaunawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya ce yanzu lokaci ya yi da za a fahinci ko za a iya cimma yarjejeniya da kasar Iran kan shirinta na nukiliya ko kuma a’a.
Wallafawa ranar:
Kerry, wanda ke zantawa da manema labarai dazun nan a birnin Vienna na kasar Austria inda kasashen duniya ke tattaunawa kan wannan batu, ya ce abu ne mai yiyuwa tattaunawar wadda za ta kawo karshe ranar 7 ga wannan wata na yuli ta haifar da sakamako nagari ko kuma akasin hakan.
A wannan lahadi wata tawaga ta manyan jami’an Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta duniya IAEA, za ta isa birnin Tehran domin ganawa da manyan jami’an kasar ta Iran kan wannan batu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu