Isa ga babban shafi
Brazil

Za a fara hukunta masu shekaru 16 a Brazil

Majalisar dokokin Brazil ta amince da dokar fara hukunta wanda ya aikata laifi daga shekaru 16 sabani shekaru 18 a kasar.Wannan dai na zuwa ne bayan kammala Jefa Kuri’ar sauya kudin tsarin mulkin kasar da ‘yan majalisun suka gudanar.

Shugabar Brazil Dilma Rousseff.
Shugabar Brazil Dilma Rousseff. Reuters/路透社
Talla

Dokar da ya samu rinjaye kuri’u 323 sama da 155 na wadanda basa goyon bayan dokar, na nufin daga yanzu duk wani mai shekara 16, za a hukunta shi idan ya aikata ko wani irin laifi, sabani adaddin shekaru da kasar ke amfani da shi a baya wato 18 wajen hukunci.

Samar da wannan doka a gwamnatin Dilma Rousseff, ya biyo bayan karuwar aikata mugan laifuka ne a cikin kasar wanda ya hada da aikata Fyade, kisa da sauransu tsakanin yara ‘yan kasa da shekaru 17.

Sai dai kuma Majalisar dinkin duniya da ma Kocin Katholikan kasar basa goyon bayan wannan sabon tsarin.

Rahotannin sun ce, ko a kwana baya an cafke wani yaro dan kasa da shekaru 17 a Rio De janeiro da laifin aikata kisa, lamarin da yasa wannan doka samun shiga a cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.