Isa ga babban shafi
Iran

An tsawaita wa’adin tattauna Nukiliyar Iran

Kasar Iran da kasashen da suke tattaunawa kan shirin nukiliyar kasar sun kara wa’adin kulla yarjejeniya daga jiya 30 ga watan Yuni zuwa ranar 7 ga watan Yuli.

An tsawaita wa'adin Tattaunawa akan Nukiliyar Iran zuwa 7 ga Yuli
An tsawaita wa'adin Tattaunawa akan Nukiliyar Iran zuwa 7 ga Yuli MEHR
Talla

Ministan harkokin wajen Russia Sergei Lavrov da ya halarci taron a Vienna ya bayyana fatar ganin an kawo karshen tattaunawar da aka kwashe shekaru biyu ana yi don samo mafita kan rikicin nukiliyar Iran na shekaru 13.

Lavrov ya ce akwai alamun cim ma biyan bukata akan tattaunar da Iran ke yi da manyan kasashen duniya da suka kunshi Amurka da Faransa da Birtaniya da Rasha da China da Jamus.

Ana sa ran a yau Laraba Sakataren Harakokin wajen Amurka John Kerry zai yi wata ganawa ta musamman da takaransa na Iran Mohammad Javad Zarif.

Manyan kasashen na son Iran da jingine shirinta na mallakar Makaman Nukiliya domin cire takunkuman da suka kakaba wa kasar.

Amma Isra’ila na ci gaba da bayyana fargaba da nuna adawa da tattaunawar da manyan kasashen ke yi da Iran.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.