Isa ga babban shafi
Faransa-Amurka

Amurka na leken asirin tattalin arzikin Faransa

Kafofin Yada labaran Faransa sun ce hukumar leken asirin Amurka ta sha sauraran wayar ministocin tattalin arzikin Faransa da kuma manyan kanfanonin kasar, wannan dai na zuwa ne kwana kalilan bayan shafin Wikileaks ya kwarmato cewa Amurka ta nadi zantukan shugabanin Kasar.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Charles Platiau
Talla

Rahotan da aka samu daga Dandalin Wikkileaks ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da tsohon ministan kudi, Pierre Moscovici wanda yanzu haka kwamishina ne a kungiyar kasahsen Turai, sai kuma Francois Baroin, ministan kasafin kudi a karkahsin shugaba Nicolas Sarkozy.

Jaridar Liberation ta Faransa ta ce Amurka ta sanya ido kan manyan kanfanonin Faransa 100, wadanda suka hada da na sadarwa, wutar lantarki, iskar gas, man fetur, nukiliya da harkokin lafiya.

A makon da ya gabata ne dai, shafin wikileaks ya kawarmato cewa Amurka ta nadi zantukan tsoffin shugabannin Faransa guda biyu Jacques Chirac da Nicolas Sarkozy, da kuma shugaba mai ci na yanzu Francois Hollande.

Al’amarin dai bai yi wa Faransa dadi ba, musamman yadda ta ke kallon Amurka a matsayin aminiyarta.

Mai Shafin wikileaks Julian Assange ya ce yanzu lokaci ya yi da ya kamata kasashen Turai su dauki matakin shari’a akan aikin leken asirin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.