Isa ga babban shafi
China

Kasashe 50 sun amince da sabon Bankin zuba jari na China

Wakilan Kasashe 50 sun sanya hannu kan yarjejeniyar kafa bankin bunkasa ayyuka da zuba jari da kasar China ke jagoranta a wani biki da aka yi a Beijing. Ana saran Bankin ya samu jarin Dala biliyan 100 wanda zai fito daga kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar.

Shugaban China Xi Jinping na jagorantar taron wakilan kasashe 50 a Beijing kan batun yarjejeniyar kafa Bankin zuba Jari na duniya
Shugaban China Xi Jinping na jagorantar taron wakilan kasashe 50 a Beijing kan batun yarjejeniyar kafa Bankin zuba Jari na duniya REUTERS
Talla

China ke da kashi 30 na hannun jarin Bankin, sai India mai kusan kashi takwas da rabi da Rasha da ke da kashi shida da rabi.

Jamus da Faransa da Brazil na daga cikin ma su jari a Bankin, yayin da Amurka da Japan suka ki sanya hannu a yarjejeniyar.

Sabon Bankin na China zai yi karo da Bankin duniya na Amurka da Bankin raya kasashen Asiya.

Bankin kuma ya hada kasashe da dama daga Nahiyoyin duniya biyar da suka hada Afrika ta kudu a Nahiyar Afrika da manyan kasashen Nahiyar Turai, Jamus da Faransa da Birtaniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.