Isa ga babban shafi
Amurka

Kotu ta halatta auren jinsi a fadin Amurka

Kotun Koli a Amurka ta Hallata auran jinsi guda a fadin kasar a yau Juma’a, matakin da aka jima ana takaddama bayan takaita dokar a wasu Jihohin kasar. Shugaba Barack Obama, ya ce matakin wata gagarumar nasara ce ga kasar Amurka baki daya.

Kotu ta hallata auren jinsi a fadin Amurka
Kotu ta hallata auren jinsi a fadin Amurka
Talla

Haka na nufin duk mai sha’awar auren jinsi guda na iya yi ba tare da wata tsangwama ba a Amurka.

Sai dai akwai wasu Amurkawa da dama da ke adawa da tsarin, musamman Alkalin Alkalai na Jihar Texas inda aka haramta auren jinsi guda.

Babu dai wata doka ko tsari da zai sauya gaskiyar aure tsakanin Mace da Namiji inda nan ne hanyar da ake samun iyali, a cewar Ken Paxton Alkalin alkalan Texas

Amma Kotun kolin ta ce kundin tsarin mulkin Amurka ya bukaci daukacin jihohin kasar da su daura auren jinsi guda kuma su amincewa da ma su yi.

Tuni dai shugaban Amurka Barack Obama mai goyan bayan hukuncin ya yaba da matakin da kotun ta dauka, inda ya ce babban Nasara ce a gwamnatinsa da masu goyan bayan tsari da suka dau tsawon lokaci suna fatan ganin wannan doka ta samu karbuwa.

Ana ganin amincewa da dokar, Shugaba Obama zai kara samun farin jini, lura da cewa tun a lokacin yaki neman zabensa na farko da na biyu ya ke da ra’ayin ganin wannan tsari ya samu zama a Amurka.

Tuni dai wadanda sukayi na’am da tsarin suka fara bayyana farin cikinsu, da murna cewa yanzu babu mai hanasu cin Karensu ba babaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.