Isa ga babban shafi
Vatican

Fafaroma ya bukaci a dauki matakai kan matsalar sauyin yanayi

Shugaban darikar Katolika, Fafaroma Francis ya bukaci a gaggauta daukar matakai domin magance matsalar sauyin yanayi, tun kafin ta haifar da ta’adi duniya baki daya. Fafaroma ya bukaci kasashe ma su karfin tattalin arziki su mayar da hankalin su wajen magance matsalar.

Fafaroma Francis shugaban Darikar Katolika
Fafaroma Francis shugaban Darikar Katolika Reuters/ Max Rossi
Talla

 

A wata sanarwar da Fadar katolika ta fitar, Fafaroma Francis ya alakanta yanayin halayar mutane da kuma rashin mayar da kai daga fannin shugabannin a matsayin babban jigo da ke barazana ga muhalli tare da haifar da matsalar sauyin yanayi.

Fafaroma na gani cewar, matsalar muhalli baya rasa nasaba da ayyukan da al’umma ke yi, don haka ya zama dole ayi gyara kafin a shawo kan matsalar.

Kalaman paproma ya sanya, ita ma babban Jami’a a hukumar kula da sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya Christiana Figueres ke yin kira da babba muryar, kan ayi amfani da kalaman Fafaroma kuma ya zama abin da za su cimma yarjejeniya akai a taron sauyin yanayi da za a gudanar a birnin paris nan gaba.

Duk da wannan kira, wasu dai na ganin cewar sauyin yanayi ba halayyar mutane kawai ke haifar da shi ba, akwai wasu abubuwa da har yanzu masana ba su gano ba
Christiana Figueres ta kara da cewa amfani da kalaman Fafaroma Francis zai taka muhimmiyar rawa wajen bada kariya daga barazanar da sauyin yanayi ke yi a kasashen duniya da dama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.