Isa ga babban shafi
G7-Najeriya

Taron G7 na kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya

Shugaban Amurka Barack Obama ya isa kasar Jamus domin halartar taron shugabannin kasashen 7 masu karfin tattalin arziki a duniya wato G7 wanda za a buda a yau lahadi.

Shugaban Amurka Obama, ya isa Jamus don taron G7 yuni 2015
Shugaban Amurka Obama, ya isa Jamus don taron G7 yuni 2015 REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Shugabar gwamantin Jamus Angela Merkel ce dai ta karbi Obama yayin da sauran shugabannin kasashen duniya ke ci gaba da isa a yankin Elmau inda za a gudanar da taron.

Daga nahiyar Afirka ma dai akwai shugabannin da aka gayyata domin halartar wannan taro da ke tattaunawa manyan batutuwa da suka shafi tattalin arziki tsaro da dai sauransu, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na daga cikin wadanda ke halatarta taron.

A nasu bangarori kuwa kungiyoyi masu yaki da tsarin jari hujja na gudanar da zanga-zangar adawa da taron na G7.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.