Isa ga babban shafi
Bosnia

Paparoma Francis ya sauka a birnin Sarajevo na kasar Bosnia

Yau Asabar Paparoma Francis isa birnin Sarajevo, a wata ziyarar wuni 1 a kasar Bosnia, inda ake fatan zai dora tubalin sasanta tsakanin Sabiyawa, Musulmi da ‘Yan Croashiya. Ziyarar ta birnin Sarajevo na zuwa ne shekaru 20, bayan yakin da aka gwabza a kasar ta yankin Balkans tsakanin shekarun 1992-95, lamarin da ya kawo rarrabuwar kanun kabilunta.Ana sa rai kimanin mutane 20,000 akasarinsu mabiya darikar Katolika, ake sa rai zasu je kasar ta Bosnia daga Croatia mai makwabta da ita.Ziyarar na zuwa ne kimanin wata guda bayan wani dan kasar mai tsananin kishin Islama ya bindige dan sanda har lahira, ya kuma raunata wasu 2, a wani harin da ya kai a arewacin kasar. 

Paparoma Francis, lokacin da ya isa birnin Sarajevo
Paparoma Francis, lokacin da ya isa birnin Sarajevo REUTERS/Max Rossi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.