Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Ukraine : Amurka na fargaba akan Rasha

Shugaban Amurka Barack Obama ya zargi kasar Rasha da kara matsa-kaimi dangane da muradunta kan rikicin kasar Ukraine. Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Obama ya tattauna da shugaban kungiyar tsaro ta NATO game da rikicin na Ukraine da ya yi sanadin utuwar mutane sama da dubu shida.

Shugaban Amurka Barack Obama yana ganawa da Shugaban NATO Stoltenberg
Shugaban Amurka Barack Obama yana ganawa da Shugaban NATO Stoltenberg © Reuters
Talla

Shugaba Obama ya gana ne da shugaban Nato Jens Stoltenberg dangane da rikicin kasar Ukraine a jiya Talata, kuma sun tattauna kan barazanar Rasha da suke zargi tana marawa ‘Yan tawaye baya da ke ra’ayin muradunta sabanin na kasashen yammaci.

Obama da shugaban NATO sun nanata bukatar Rasha ta mutunta yarjejeniyar watan Fabrairu ta tsagaita wuta da aka yi watsi da ita.

Shugaban NATO ya ce yarjejeniyar ce kawai za ta kai ga samun cikakken zaman lafiya tsakanin bangarorin da ke rikici a Ukraine.

Amurka tare da Manyan kasashen Turai sun amince da yarjejeniyar ne tsakaninsu da Rasha da kuma Ukraine domin kawo karshen rikicin da aka shafe sama da shekara ana zubar jini.

Akalla mutane sama da dubu shida suka mutu tare da raba mutane sama da miliyan da gidajensu.

Amurka dai na zargin Rasha ne da marawa ‘Yan tawaye baya tare da ba su makamai, zargin da kuma Rasha ke musantawa.

A watan Yuni ne NATO za ta yi taro don tattauna rikicin Ukraine da kuma barazanar Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.