Isa ga babban shafi
Colombia

Rikici ya barke tsakanin 'Yan tawayen FARC da sojan gwamnatin Colombiya

Tattaunawar neman zaman lafiya, don kawo karshen rikicin da aka shafe fiye da shgekaru 50 ana yi a kasar Colombiya ta shiga garari a jiya juma’a, bayan da ‘yan tawayen FARC suka ce sun fice daga yarjejeniyar. Mayakan sunkurun, sun dauki wannan matakin ne, bayan da dakarun gwamnati suka kai musu harin sama, inda aka kashe ‘yan tawayen 26.Sanarwar tsagaita wuta da ‘yan tawayen suka bayar a watan Disamban bara, ta sanya fatan samun dawwamammen zaman lafiya, sai dai kuma kwanton bauna da wasu mayakan suka yi, inda suka kashe sojojin Colombiya 11, ya haifar da rashin tabbas. 

Sojan kasar Colombiya suna kwawar da wasu gawarwaki
Sojan kasar Colombiya suna kwawar da wasu gawarwaki REUTERS/Jaime Saldarriaga.
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.