Isa ga babban shafi
Haiti

Alkallumar Cutar cholera na karuwa a Haiti-MDD

Majalisar dinkin duniya ta ce alkalluma cutar Cholera na karuwa a kasar Haiti, inda a yanzu daruruwan al’ummar kasar na kamuwa da cutar a duk sati.Rahotanin dai na cewa kokarin da hukumomi keyi domin dakile cutar baya yiwuwa, saboda karanci masu bada agaji.

Sojoji da ke bada taimako a Haiti
Sojoji da ke bada taimako a Haiti USAF
Talla

Mai kula da shirin yaki da cutar cholera na MDD a Haiti Pedro Medrano yace rashin kayayyaki agaji, da kuma yanayin damina, tsahon watanin 6 baya, ya sanya karuwar alkallumar mutane da ke dauke da cutar Cholera a kasar

Pedro yace a baya a duk wata guda ana samu mutane dubu dauke da cutar, amma a yanzu a duk sati ake samun mutane kusan dubu dauke da cutar

Pedro ya kuma yi hasashen cewar lura da yanayi da ake ciki a yanzu, alkallumar masu dauke da cutar ka iya zarcewa dubu 50 acikin shekarar na, sabanin dubu 28 da aka samu a shekarar da ta gabata

Cutar cholera ta kasha mutane kusan dubu 9 a Haiti, tun daga lokaci da ta barke acikin shekrara ta 2010, yayyin da mutane dubu 736 suka kamu da cutar, cutar da kwararru ke zargin dakarun kasar Nepal da yadda ta a cikin kasar

A yanzu dai kasar Haiti na fama da karanci kayayyakin agajin gagawa, da jami’an kiwon lafiya, da asibitoci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.