Isa ga babban shafi
Nepal

MDD ta kaddamar da gidauniyar taimakawa Nepal

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar Dala miliyan 415 don tallafawa al’ummar kasar Nepal da girgizar kasa ta daidaita, a dai dai lokacin da adadin wadanda suka mutu ya kai 5,489. Rahotanni sun ce kayan agaji na karewa, yayin da wadanda bala’in ya shafa ke dada shiga halin kunci, yayin da mutane sama da miliyan biyu da rabi suka rasa matsuguni.

'Yan sandan Nepal na arangama da masu bore.
'Yan sandan Nepal na arangama da masu bore. Reuters
Talla

Dubban mutanen ne suka yi tururuwa a tashar motocin kasar suna shirin barin kasar sakamakon alkawarin da gwamnati ta yi cewar za ta samar da motocin safa safa, amma rashin ganin motocin ya sa jama’a bore da arangama da ‘Yan Sanda.

Rahotanni sun ce wasu ‘yan kasar sun kai ga shan fitsarinsu saboda matsanancin rashin ruwan sha da abinci a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya tace adadin wadanda suka mutu sakamakon girgizan kasar ya zarce mutane 5000, yayin da daruruwa suka samu rauni.

Kungiyoyin agaji na kasashen duniya da dama na ci gaba da kai kayan agaji ga dubban mutanen da bala’in girgizar kasar Nepal ya shafa a kauyuka da Kathmandu babban birnin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.