Isa ga babban shafi
Amurka-Cuba

Obama ya gama hannu da Castro a Panama

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya gama hannu da takwaransa na Cuba Raul Castro a taron kasashen yankin America da ake gudanarwa a Panama bayan kasashen biyu sun shafe shekaru suna gaba da juna. Wannan ne karo na farko da shugaban kasar Cuba ya ziyarci taron kasashen.

Raul Castro na Cuba yana gaisawa da Barack Obama na Amurka
Raul Castro na Cuba yana gaisawa da Barack Obama na Amurka REUTERS/Panama Presidency
Talla

Kafin su zauna a zauren taron a Panama, shugabannin biyu sun zanta da juna.

Obama da Raul Castro sun taba gama hannu a Johannesburg wajen Jana’izar tsohon Shugaban Afrika ta kudu Nelson Mandela a 2013.

Haduwar kasashen biyu dai ana ganin mataki ne na kokarin farfado da huldar diflomasiya tsakanin kasashen biyu da ke gaba da juna tun 1961.

A yau Assabar ana sa ran Obama zai gana da Castro akan batutuwan diflomasiya da ya kunshi bude ofishin jekadancinsu.

Ana sa ran kuma Obama zai yi amfani da damar taron ya tattauna da wasu kasashen Latin da ke da sabanin ra’ayi da Amurka.

Obama zai tattauna da shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos da shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff wacce ta katse kai ziyara Amurka saboda zargin Jami’ar leken asirin kasar na nadar bayananta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.