Hadarin Jirgin Sama a Faransa shine mafi muni cikin shekeru 30
Hukumomi a kasar Faransa sun bayyana hatsarin saman da ya auku a cikin kasar, a matsayin wanda ya fi lakume rayuka shekaru sama da 30 da suka gabata, a yayin da Shugaban Kasar, Francois Hollande, ya jaddada kudirin gano musabbin hadarin
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tun shekara ta 1974, da jirgin Turkiya ya yi hadari a Faransa, inda mutane 346 suka rasa rayukansu, a karo na farko kenan da mafi munin hadarin jirgin sama ya auku a kasar.
Shugaban Kasar, Francois Hollande, ya jaddada Kudirinsu na tabbatar da cewa sun gano musabbain aukuwar hadarin, inda akasarin fasijojin dake cikin jirgin ‘Yan asalin kasashen Jamus ne, Spain da Turkiya, kuma akwai jarirai biyu a ciki baya ga daliban makaranta 16.
Gabanin faruwar lamarin, hukumar kula da zirga-zairgar jiragen Sama ta Faransa, ta sanar cewa, ta daina jin duriyar jirgin bayan matsalar da aka samu ta katsewar hanyar sadarwa tsakaninta da jirgin.
Tuni dai shugaban Amurka, Barrack Obama ya aike da sakon ta’aziya ga kasashen da lamarin ya shafa, inda yace, jami’ansu na gudanar da bincike dan gano ko akwai ‘Yan Kasar Amurka a cikin hadarin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu