Isa ga babban shafi
Vanuatu

Kasashen duniya sun fara kai dauki zuwa tsibirin Vanuatu

Kungiyoyin bada agaji na cigaba da aikewa da kayayyakin agaji zuwa yankin Vanuatu dake tsubirin Pacific inda mahaukaciyar iska da ruwan sama ta yi mummunan barnan a karshen mako.Ya zuwa jiya lahadi dai Hukumomin yankin sun bayyana dokar ta baci ganin irin barnar da mahaukaciyar iskar da ruwan sama suka yi, inda bayanai ke nuna cewa matsalar ta yi sanadiyya shafe kauyuka da dama daga doron kasa.An ce mutane 6 suka mutu a Port Vila, babban birnin yankin, koda yake kungiyoyin agaji sun ce mamata a fadin kasar nada yawan gaske.Rahotanni ne cewa akasarin hanyoyin sadarwan a yankin duk sun katse, amma duk da haka an bude filin jiragen sama na Port Vila domin karban kayan agaji daga sassan duniya.An ga wasu jiragen saman sojan kasar Australia biyu, shake da kayan abinci, magunguna da kayan rufa sun sauka a birnin, sannan kuma akwai wani jirgin saman soja na kasar New Zealand cike da tampol na yin rumfuna, da jarkunan ruwan sha, dasu injin bayar da wutar lantarki wato janareto da za a rabawa jama’a dake cikin wani hali.Shugaban kasar kasar Vanuatu Baldwin Lonsdale ya mika kokon barar sa ga kasashen duniya dasu taimakawa kasar tasa mai yawa mutane dubu 270. 

Mahaukaciyar iska tayi ta'adi a Vanuatu
Mahaukaciyar iska tayi ta'adi a Vanuatu REUTERS/UNICEF Pacific/Handout via Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.