Isa ga babban shafi

Amurka ta nemi a kawo karshen hare hare a birnin Jerusalem

Sakataren harkokin wajen Amurka john kerry yayi Allah wadai, da harin da aka kai da wata motar a birnin Jerusalam, inda ya bayyana lamarin da hari irin na taadaci, da ka iya cigaba da haifar da zaman dar dar a yankin, dake fama rikice rikice.A lokacin da yake wa yan jaridu bayyani kafin haduwa su da ministan harkokin waje kasar Jordan a birnin Paris, Mr Kerry yace irin wanna hare hare na dawo da hannun agogo ba, a kokarin samar da zaman lafiya.Kerry yayi kira tare da jan kunen al’umma dasu yi kokarin samar da zaman lafiya a yanki da ake fama da fitintinu.A dai safiyar laraba ne wani Bapalasdine ya kutsa motar sa a cikin masu wucewa da kafa a birnin Jerusalam, wanda yayi sanadi mutuwar dan sanda guda tare da jikata mutane 9, kuma wanna shine karo na biyu da aka kai irin wanna hari acikin makonnin da suka gabata.Wanna lamari yayi sanadi haifar da tarzoma a maasallaci Al Aqsa tsakanin jami’an tsaro da matasan Palasdinawa, dake jifar ‘yan sandan da duwatsuMinistan harkokin wajen kasar Jordan Nasser Judeh yace daya daga cikin hanyoyi da za a iya bi wajen shawo kan wanna matsala iatace sassanta rikici kasashen Larabawa da Isara’ila. 

Sakataren harkokkin wajen Amurka John Kerry.
Sakataren harkokkin wajen Amurka John Kerry. REUTERS/Gary Cameron
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.