Cuba
Kotu ta daure Malaman da suka sayar da Jarabawa a Cuba
Wata kotu a kasar Cuba ta yanke hukuncin daurin shekaru takwas ga wasu Malaman Jami’a guda bakwai da aka samu da laifin sayar da jarabawar shiga Jami’a. Jaridar Granma a kasar tace Malaman sun saci takardun Jarabawar a watan Yuni tare da sayarwa akan dala 180.
Wallafawa ranar:
Talla
Ana bayar da ilimi kyauta ne a kasar Cuba, amma dole sai dalibai sun samu sakamako mai kyau kafin su shiga Jami’a.
Bayan yanke wa Malaman hukunci, kuma Kotun ta kori su daga aikin Malamanta tare da umartar su biya diyya ga Ma’aikatar ilimi da kuma Jami’ar Havana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu