Isa ga babban shafi

An fara hada hada a cibiyar kasuwanci ta birnin New York

Katafaren benen nan da ya fi ko wane bene tsawo a birnin New York na kasar Amruka wato World Trade Center, da aka gina a wajenda ‘yan tagwayen benayen nan na cibiyar kasuwanci ta duniya, da harin ranar 11 ga watan Satumbar 2001 ya rusa, ya buda kofofinsa ga masu haya na farko a jiya litanin. A kalla mutane 175 ne dake rike da mukaman daraktoci da suka hada da gungunan na kasar Amruka masu buga majallu ta le New Yorker da Vanity Fair, sun suka fara saka kafa a sabon gini a matsayin masu haya, a jiya litanin.Wani jami’in kamafanin Condé Nast, John Duffy, ya bayyana cewa shugabanninsu ne suka fara komawa a sabon ginin domin bada misali domin kuma nuna cewa suna bukatar ci gaba da kasancewa a ginin domin gudanar da ayukansuWasu daga cikin mutane na cike da fushi ne a yayinda wasu ke cike da farin ciki kan komawa ginin dake yankin kudancin birnin New YorkA ranar 11 Satumban shekarar 2001, harin ta’addancin da aka kai a kan yan tagwayen gine ginen cibiyar kasuwancin ta duniya, ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2,753 wanda ya bar wani tabo marar goguwa ga birnin da ma kasar ta Amruka baki daya.Cibiyar ta kasuwanci na da tsawon mita 541,30 kuma ginin na kunshe da hawa 104 shahararen mai zana taswirar gini nan ne David Childs ya zana shi. Ginin dai mallakar hukumar Durst Organization ne mammalakin tashoshin jiragen ruwan birnin New York da New Jersey, hukumar da ta kasance mallakar gwamnatin kasar Amruka. 

Cibiyar kasuwanci ta duniya dakebirnin New York
Cibiyar kasuwanci ta duniya dakebirnin New York REUTERS/Shannon Stapleton
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.