Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra’ila ta yi hasarar kudi Biliyan biyu da rabi a rikicin Gaza

Kasar Isra’ila tace ta kashe kudi har Dala biliyan biyu da rabi wajen yakin Gaza, wanda ya kai ga kashe Falasdinawa sama da 2.000. Ministan tsaron kasar Moshe Yalon ne ya bayyana haka yana mai cewa sun kai hare hare sau 6,000, kuma sama da 5,000 daga cikin su harin sama ne da hare hare ta kasa 900.

Mazauna garin Gaza a cikin gidansu da hare haren Isra'ila suka tarwatsa.
Mazauna garin Gaza a cikin gidansu da hare haren Isra'ila suka tarwatsa. REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Yalon yace duk da ruwan wutar da suka yi wa Hamas a Gaza, amma har yanzu Hamas tana da makaman roka aje, bayan sama da 10,000 da ta dinga cillawa zuwa cikin Isra’ila.

A cewar Ministan sun ci riba a kudaden da suka kashe a rikicin gaza saboda yadda suka lalata makaman roka da Hamas ke cillawa.

Amma yanzu haka gwamnatin Isra’ila tace zata datse kasafin kudinta domin cike gibin kudaden da ta kashe a rikicin Gaza.

Sojojin Isra’ila dai kusan 70 ne aka kashe a rikicin da aka kwashe tsawon kwanaki 50 ana luguden wuta a Gaza, kafin cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.

A yau Laraba ne kuma Sakataren harakokin wajen Amurka john Kerry zai gana da wakilan Falasdinawa a Washington domin tattauna batun dorewar yarjejeniyar tsagaita wuta da wasu batutuwa da suka shafi rikicinsu da Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.