Isa ga babban shafi
IATA

Hukumar Zirga-zirgar Jirage za ta dauki matakai

Hukumar zirga-zirgar Jiragen sama ta duniya tace zata dauki matakan kare aukuwar hadarin Jirage bayan faduwar Jirage guda uku da suka yi sanadin mutuwar mutane 460 a cikin ‘yan kwanakin nan.

Wasu Tarkacen Jirgin Malaysia MH17 da ya fado a gabacin kasar Ukraine
Wasu Tarkacen Jirgin Malaysia MH17 da ya fado a gabacin kasar Ukraine Reuters
Talla

A cikin wata sanarwa, shugaban Kungiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta duniya Tony Tyler yace ya yi imanin mutane zasu fara sa alamar tambaya ga sha’anin Jirage a duniya, saboda hadurran da suka faru da jirage na kasashen Malaysia da Taiwan da Algeria.

Hukumar ta jajantawa ‘Yan uwan wadanda suka mutu tare da shan alwashin daukar matakai domin kare aukuwar hadurran jirage a duniya.

A ranar 17 ga watan Yuli ne jirgin Malaysia ya yi hadari a gabacin Ukraine, inda ake zargin ‘Yan tawayen kasar ne suka harbo jirgin mai dauke da mutane 298.

A ranar Laraba ne kuma Jirgin Taiwan ya yi hadari a gabacin kasar inda mutane 48 suka mutu.

A ranar Juma’a ne kuma aka gano tarkacen Jirgin Algeria da ya fado a arewacin Mali dauke da mutane 116 a cikinsa bayan ya taso daga Burkaina Faso zuwa Algeria.

Mista Tyler yace adadin wadanda suka mutu a bana sun zarce na bara inda aka samu mutuwar mutane 210 sakamakon hadarin jirage.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.