Isa ga babban shafi
Ukraine-Malaysia

MH17: ‘Yan tawayen Ukraine sun ga akwatin nadar bayanai

‘Yan tawaye masu kishin Rasha da suka mamaye gabacin Ukraine sun ce sun gano bakin akwatin nadar bayanai na jirgin Malaysia wanda ya tarwatse a yankin da suke iko, kuma sun ce a shirye suke su mika wa tawagar masu bincike, akwatin domin gudanar da bincike.

Wani Dan tawayen Ukraine a yankin da jirgin Malaysia ya tarwatse.
Wani Dan tawayen Ukraine a yankin da jirgin Malaysia ya tarwatse. ©REUTERS/Maxim Zmeyev
Talla

Shugaban ‘Yan tawayen da ke kiran kasa Firaministan Jamhuriyyar mutanen Donetsk Alexander Borodai yace idan tawagar masu gudanar da bincike suka iso zasu mika masu akwatin.

Ana zargin ‘Yan tawayen na Ukraine da boye wasu hujjoji da zasu tabbatar da harbo jirgin Malayasia MH17 aka yi da makami mai linzami a yankin da suke iko.

A yau Lahadi, manyan kasashen Turai Faransa da Birtniya da Jamus sun yi gargadi ga Rasha ta tursasawa ‘Yan tawayen su ba masu bincike damar isa ga yankin da jirgin ya tarwatse, idan ba haka ba su tsaurara wa Rasha takunkumi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.