Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka-Turai

Ukraine: Putin ya yi kakkausar suka kan manufofin Amurka

Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya dora laifin rikicin Ukraine akan kasashen yammaci, lamarin da ya kwatanta a matsayin yunkurin haddasa gaba tsakanin kasarsa da kawayenta na asali a nahiyar turai.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/Maxim Zmeyev
Talla

Putin ya bayyana hakan ne yayin da yake zayyana muhimman batutuwan da suka shafi harkokin wajen kasarsa.

Masana harkokin siyasa sun kwatanta wannan jawabi a matsayin wani yunkuri na haifar da rashin jituwa tsakanin hukumomin Brussels da Fadar Washington.

Shugaba Putin wanda jawabin shi yafi mayar da hankali kan kasar Amurka, ya bayar da misalin yadda Amurkan ta ke tsanantawa bankunan Faransa a yunkurin da Faransan ken a sayarwa da Rasha tankunan yaki.

Putin ya kuma bayyana cewa ‘yan siyasa da ‘yan kasawa da dama daga nahiyar ta turai sun gano cewa, ana so ne kawai a yi amfani da su wajen cim ma wata manufa da bata shafe sub a.

Ya kuma jaddada cewa Rasha, kasa ce da nahiyar Turai ba za ta iya yanke hulda da ita ba, duk irin barazanar karin takunkumai da kasashen yammaci ke shirin kakaba mata.

Wannna jawabi na Putin na zuwa ne jim kadan bayan da yunkurin kara tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Ukraine ya gagara duk da goyon bayan da kungiyar tarayyar turai da hukumomin Moscow suka nuna.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.