Isa ga babban shafi
Bosnia

Dalilin faruwar yakin Duniya na farko

Mutanen Bosnia suna bikin cika shekaru 100 da kisan Archduke Franz Ferdinand, Yariman Austria a birnin Sarajevo a shekara ta 1914, al’amarin da ya yi sanadin haifar da yakin duniya na farko.

Mutum Mutumin Gavrilo Princip, wanda ya bindige archiduke François Ferdinand a Sarajevo babban birnin kasar Bosnia a 1914.
Mutum Mutumin Gavrilo Princip, wanda ya bindige archiduke François Ferdinand a Sarajevo babban birnin kasar Bosnia a 1914. REUTERS/Dado Ruvic
Talla

A tsakiyar birnin Sarajevo ne wani dan Yugoslavia dan kishin kasa mai suna Gabrilo Princip ya bindige Archduke Franz Ferdinand da Matarsa, lamarin da ya jefa duniya  cikin yaki na tsawon shekaru hudu.

Sai dai kuma akwai rabuwar kai tsakanin mutanen Balkans da suka hada da Sabiyawa da Musulmin Bosnia da sauran kabilun yankin game da al’amarin. Wannan ne kuma ya hanawa shugabannin yankin haduwa a waje daya domin gudanar da bikin a yau Assabar.

A kasar Austria ma Jikoki da dangin Franz Ferdinand da aka kashe zasu gudanar da bikin tunawa da kisan shi yau tsawon shekaru 100.

Sabiyawa dai sun dauki Gavrilo Princip a matsayin Jarumi wanda ya kwato masu ‘yanci inda wasu Sojojin Serbia ke bauta masa, amma Musulmin Bosnia suna ma shi kallon Dan ta’adda.

Bayan kammala yakin duniya na farko sai da aka sake fasalta taswirar duniya saboda faduwar manyan daulolin Rasha da Jamus da daular Ottoman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.