Isa ga babban shafi
China-Syria-Rasha

Rasha da China sun hau kujerar na-ki akan Syria

Kasashen China da Rasha sun hau kujerar na-ki kan yunkurin Majalisar Dinkin Duniya na gurfanar da Syria a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, saboda laifukan da aka tafka a yakin basasan da aka shafe shekaru uku.

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na China Xi Jinping
Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na China Xi Jinping Reuters
Talla

Manyan kasashen yammacin duniya ne ke neman a gurfanar da dukkan bangarorin biyu, saboda zargin aikaita laifukan da suka hada da amfani da makamai masu guba, azabtarwa da daste hanyoyin kai agaji ga mabukata.

Tuni kungiyar kare hakkin da Adam ta Amnesty Internetional ta yi Allah wadai da wannan matakin, tare da zargin kasashen China da Rasha da kawar da kai daga bala’oin da ‘yan kasar ta Syria ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.