Bosnia
ICC: Mladic zai fara kare kansa akan yakin Bosnia
Yau Litinin ake saran Janar Ratko Mladic da ake zargi da aikata laifukan yaki a kotun duniya zai fara kare kansa daga zargin kisan kiyashin da ake masa a yakin Bosnia, wanda shi ne yaki da aka bayyana an aikata banna mafi muni a Turai tun kawo karshen yakin duniya na biyu.
Wallafawa ranar:
Talla
Mladic mai shekaru 71 na fuskantar laifukan yaki 11 da suka hada da garkuwa da mutane da kuma kisan kare dangi a yakin Bornia tsakanin shekarar 1992 zuwa 1995 inda aka kashe mutane sama da Miliyan 10 tare da raba mutane miliyan biyu suka muhallinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu