Isa ga babban shafi
Malaysia-Australia

Australia na fatan za a samo jirgin saman kasar Malaysia da ya bace

Yau Lahadi Priministan kasar Autraliya Tony Abbott yace suna samun karin fatan gano jirgin saman kasar Malaysia daya yi batan dabo, yau fiye da makonni 2. Priminista Abott ya fadi haka ne, bayan da jirgin saman kasar ya gano wasu bubushin da ake tunani na girgin ne, a inda ake neman jirgin kan tekun Indiya.An fara yi wa burbushin kallon kuriulla, bayan wasu sabbin hotunan da aka dauka daga tauraron dan Adam din kasar China, sun nuna wani abu na yawo a kan ruwa, a yankin da keda nisan Kilimita 2,500 a kan teku, a kudu maso yammacin birnin Perth na kasar ta Australia. 

Jirgin saman Australia, da ke aikin neman jirgin kasar Malaysia
Jirgin saman Australia, da ke aikin neman jirgin kasar Malaysia Reuters/路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.