Firaministan Faransa yana ziyara a Algeria don inganta huldar kasuwanci
Firaministan Faransa Jean-Marc Ayrault na gudanar da ziyarar aiki ta tsawon yini biyu da zai fara a yau Litinin ya kammala a gobe Talata a kasar Algeria. Ziyarar na zuwa ne shekara daya bayan da shugaba Francois Hollande ya ziyarci birnin Algers, yayin da Faransa ke ci gaba da kansacewa kasa ta farko da ke da alakar ciniki da tattalin arziki da Algeria a duniya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Faransa tana neman inganta huldar kasuwanci ne tsakaninta da Algeria domin hamayya da China.
Kawancen kasashen biyu dai yana tattare da sarkakiya, amma Faransa tana fatar farfado da huldarta da Algeria tun ziyarar Hollande a watan Disemban bara, a yayin da Firaminista Jean- Marc Ayrault ya gana da takwaransa Abdelmalek Sellal.
Daga cikin tawagar Firaministan Faransa, akwai Ministoci 9 da suka raka shi zuwa Algeria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu