Mataimakin shugaban Amurka Biden ya isa China
Mataimakin Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya isa kasar China, a cigaba da ziyarar kasashen dake Gabashin Asiya da ya ke yi yanzu haka, inda ake sa ran zai tattauna da hukumomin kasar.
Wallafawa ranar:
Kafofin yada labaran China sun gargadi Biden daya kaucewa yin kalaman da zasu tada jijiyoyin wuya a kasar, kan matakin da China ta dauka na sanya wani Yanki da suke takaddama akai da Japan a matsayin na hana shawagin jiragen sama.
A lokacin da Biden ya sauka a jirgin Beijing an ganshi yana daga hannayensa a matsayin gaisuwa yayin da wasu dakaru suka tarbe shi.
Ana sa ran daga kasar ta China, mataimakin shugaban kasar zai wuce kasar Korea ta Kudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu