Isa ga babban shafi
Panama

An ci tarar wani jirgin ruwa a kasar Panama

Hukumar kula da mashigin ruwan kasar Panama, ta ce za ta ci jirgin ruwar kasar Koriya Ta Arewa, kudi dalar Amurka miliyan daya, domin kama shi da ta yi da laifin shiga ruwan kasar da makamai, zuwa kasar Cuba ba a kan ka’ida ba. Shugaban hukumar da kula da wannan mashigi Jorge Quijano yace, jigilar makaman ya sabawa dokar kare mashigin ruwa, kuma ba za su yarda da irin wadanann ayyukan ba.Ya ce dole ne a hukuntar da su, ya kara da cewar kawo yanzu akwai wasu sundukai, dauke da kaya a cikin wannan jirgi daukar kaya wadanda har yanzu ba a bayana abubuwan da suke dauke da su ba.To sai dai binciken da hukumomi suka yi ya ba su damar gano wasu sundukan guda 25 da ke dauke da kayan aikin soja, da suka hada da makamai kirar kasar Rasha, da makamai masu linzame, da manyan motocin yaki, wadanda aka boye a karkashin jikunan sukari.Wannan mataki da hukumomin kasar ta Panama suka sanar, na zuwa ne a daidai lokacin da wata tawagar kwararru ta Majalisar Dinkin Duniya, ta isa a kasar domin gudanar da bincike kan wannan batu. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.