Isa ga babban shafi
Pakistan-Amurka

Bin Laden ya kwashe tsawon shekaru 9 a Pakistan kafin a kashe shi-Rahoto

Wani Rahoton bincike na Sirri kan yadda Amurka ta kashe Osama bin Laden, rahoton yace shugaban na al Qaeda ya kwashe tsawon shekaru 9 a Pakistan tare da dora laifin ga gwamnatin Islamabad a matsayin sakaci da Gazawa da har shugaban zai kwashe tsawon shekaru ba tare da sun gano mabuyar shi ba.

Marigayi Osama Bin Laden wanda Dakarun Amurka suka kashe a Pakistan
Marigayi Osama Bin Laden wanda Dakarun Amurka suka kashe a Pakistan @Reuters
Talla

Rahoton wanda ya fito daga hukumar shari’a ta Pakistan, ya yi bayanin samamen da dakarun Amurka suka kai da ya ba su nasarar kashe Osama Bin Laden.

Rahotan wanda kafar yada labaran Al Jazeera ta samu kwafi, yace kashe Bin Laden a kasar, wani kisan kai ne da shugaban kasar Amurka ya bayar da umurnin aikatawa.

Rahotan ya bayyana yadda Osama ya gudanar da rayuwa a cikin kasar, tun lokacin da ya fice Afghanistan.

Dakarun Amurka sun kashe Bin Laden ne a wani gidan da ke arewa maso yammacin birnin Abbottabad, a watan Mayu na shekarar 2011.

Tun bayan kisan Osama ne, gwamnatin Pakistan ta nada kwamiti domin binciken al’amarin.

Kwamitin ya zanta da matan Bin Laden kafin su fice zuwa kasar Saudiya. Amma sakamakon binciken an ajiye ne a matsayin sirrin gwamnati kafin ranar Litinin da kafar yada labaran al Jazeera ta yada rahoton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.