Isa ga babban shafi
Bolivia

Bolivia ta soki kasashen Turai bayan haramtawa jirginta sauka

Kasar Bolivia ta bayyana bacin ranta kan yadda aka karkata akalar jirgin da ke dauke da shugaban kasar ta, Evo Morales, saboda zargin cewar jirgin na dauke da Edward Snowden da Amurka ke nema ruwa ajallo. Rahotanni sun ce, kasashen Faransa da Portugal, sun ki yar da jirgin da ke dauke da shugaba Morales, ya wuce ta cikin sararin samaniyar yankunan kasashen.

Jirgin shugaban Bolivia Evo Morales a tashar jirgin Vienna
Jirgin shugaban Bolivia Evo Morales a tashar jirgin Vienna REUTERS/Heinz-Peter Bader
Talla

Ministan harkokin wajen Bolivia, David Choquehuanca, ya zargi Amurka da kitsa karyar cewar Snowden yana jirgin shugaban.

Shugaba Evo Morales dole ya koma Bolivia daga Rasha bayan karkatar da jirgin zuwa Vienna.
Kasar Bolivia dai na cikin kasashen da suka ce za sub a Snowden mafaka wanda ya fallasa sirrin Amurka.

Kasashen da ke Amurka ta kudu da Asia da Turai, sun ki amincewa su bai wa Edward Snowden mafakar siyasa, duk da kiran da shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro ya yi, na ganin an kare shi.

Snowden ya gabatar da bukatar sa ga kasashe 21 da suka hada da India da China da Brazil da Faransa da Jamusda Italiya daHolland da Venezuela, amma akasarin kasashen sun ki amincewa da bukatarsa.

Ya zuwa yanzu dai Snowden na ci gaba da zama a tashar jiragen saman Russia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.