Isa ga babban shafi
Guatemala

An tusa keyar tsohon shugaban Guatemala Alfonso Portillo zuwa Amurka

An tusa keyar tsohon shugaban kasar Guatemala, Alfonso Portillo zuwa kasar Amurka domin gurfana a gaban wata kotun birnin New York da ke zarginsa da hannu wajen karkata akalar wasu makuddan kudade mallakin kasarsa a lokacin da ya ke kan karagar mulki.

Tsohon shugaban Gautemala, Alfonso Portillo
Tsohon shugaban Gautemala, Alfonso Portillo
Talla

Rahotanni sun ce kotun ta birnin New York na zargin tsohon shugaban kasar ne wanda ya yi mulki daga shekara ta 2000 zuwa 2004 kan cewa ya handame dukiyar kasarsa da yawanta ya kai dalar Amurka milyan 70.
Shi dai tsohon shugaba Alfonso, ya boye wadannan kudade ne a cikin wani banki da ke birnin Miami na kasar ta Amurka. Bayan saukarsa daga karagar mulki a shekara ta 2004, tsohon shugaban ya gudu ya bar kasar zuwa Mexico, to amma hukumomin kasar ta Mexico sun mayar da shi kasarsa a shekara ta 2008 domin fuskantar wasu zarge zargen rashawa da ake yi masa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.