Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 17/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 12/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 17/01 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/01 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 17/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 17/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 17/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/01 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 17/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 17/01 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 17/01 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 18/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 18/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 17/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Duniya
G8

Kofi Annan ya nemi kasashe masu arziki su tallafa wa nahiyar Africa

media Tsohon Sakkatare Janar na MDD, Kofi Annan REUTERS/Allison Joyce

Tsohon Sakateren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan ya bukaci gungun kasashe Takwas masu karfin tattalin arzikin duniya da ake kira G8 su tallafawa kasashen Afrika ta hanyar gaggauta samar da wasu sabbin matakan dakile yaduwar cin hanci da rashawa da kuma haraji da ke rarake arzikin Nahiyar. A wani rahoto da aka wallafa a yau Juma’a, Kwamitin Kofi Anan na mutane 10 da aka kafa domin duba hanyoyin ci gaban Afrika, tsohon sakataren na Majalisar Dinkin Duniyar, ya yi kira ga kasashen G8 su dinga aiwatar da gaskiya, wajen gudanar da ayyukan masana’antunsu da yadda suke tatso arzikin kasashen Afrika da ke neman yin kafada da kasashen Asiya da kuma Latin Amurka, wajen habakar tattalin arziki.
Annan ya kuma bukaci kasashen na G8 su samar da sabbin dokoki ga kamfanoninsu da kuma haraji, tare da danganta matsalar cin hanci da rashawa, da ta zama ruwan dare a gwamnatocin kasashen Afrika.

Rahoton yace akwai wasu kamfanoni da ke bin ta bayan fage domin kaucewa biyan  haraji domin samun ribar kasuwacin su, a yayin da Miliyoyan al’ummar Afrika ke cikin matsanancin halin karancin Abinci da tabarbarewa kiwon lafiya da kuma ilimi.
Gungun kasashe G8 dai sun hada da Canada da Faransa da Jamus da Italy da Japan da Rasha da Ingila da kuma Amurka.
 

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure