Isa ga babban shafi
Amurka-Iran-Isra'ila

Amurka na iya haramtawa Iran samun nasarar mallakar Nukiliya-Obama

Shugaba Barack Obama yace Amurka na iya haramtawa Iran cim ma kudirin mallakar Makamin Nukiliya, yana mai cewa akwai dubarun da zai bi idan an kasa sasantawa da Iran ta hanyar Diflomasiya.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Larry Downing
Talla

A lokacin da ake zantawa da Obama a wata kafar yada labaran Isra’ila, Shugaban ya shaidawa Isra’ila cewa Amurka tana da karfin haramtawa Iran samun nasarar mallakar Makamin Nukiliya.

A makon gobe ne ake sa ran Obama zai kai ziyara kasar Isra’ila, kuma shugaban yace Iran zata kwashe tsawon shekara ko fiye da haka kafin ta samu nasarar kammala aikin mallakar makamin Nukiliya.

Tuni dai Isra’ila ta yi barazanar kai wa Cibiyar Nukiliyar Iran hari. Sai dai Gwamnatin Iran tace shirinta na Nukiliya na zaman lafiya ne a Duniya.

Game da batun sasanta rikicin Isra’ila da Faledinawa, Obama yace zai tattauna da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kuma Shugaban Falesdinawa Mahmoud Abbas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.