Isa ga babban shafi
Venezuela

Shugabannin Duniya sun taru a Venezuela domin bukin jana’izar Chavez

Shugabannin kasashen Duniya sama da Hamsin ne ake sa ran za su halarci bukin jana’izar mutuwar shugaban Venezuela Hugo Chavez, inda shugabannin kasashe masu adawa da Amurka irinsu Iran da Cuba ke sahun gaba wajen taya dubban mutanen kasar zaman makokin shugabansu.

Marigayi Shugaban Venezuela Hugo Chavez a lokacin da ya ke wata ganawa da Shugaban Rasha Vladimir Putin à Moscow
Marigayi Shugaban Venezuela Hugo Chavez a lokacin da ya ke wata ganawa da Shugaban Rasha Vladimir Putin à Moscow AFP PHOTO / YURI KADOBNOV
Talla

Ana sa ran rantsar da mataimakin Hugo Chavez, Nicolas Maduro, a matsayin shugaban riko wanda zai jagoranci gudanar sabon zaben shugaban kasa.

Shugaban Cuba Raul Castro da shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad da shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko suna cikin shugabannin da ke adawa da Amurka da suka hallara a kasar Venezuela.

Mista Maduro ya ce za’a kwashi gawar Chavez ne zuwa wani tsauni a barikin Soji, da ake kira fadar Chavez ta juyin juya hali a kasar Venezuela inda ya jagoranci taron soji don hambarar da gwamnatin shugaba Carlos Andres Perez a ranar Hudu ga watan Fabrairun shekarar 1992.

Juyin mulkin Chavez bai samu nasara ba amma cafke Chavez shi ne ya kara masa farin jini a kasar wanda har ya yi sanadiyar ya lashe zabe a 1998.

Bayan kammala bukin jana’izar Chavez, ana sa ran shugaban majalisar kasar Diosdado Cabello, zai rantsar da Maduro a matsayin shugaban rikon kwarya.

Ana sa ran gudanar zaben shugaban kasa nan da kwanaki 30 kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.