Amurka-Jordan
Kakakin Osama bin laden zai gurfana gaban kotun Amurka
Sulaiman Abu Ghaith da aka bayyana a matayin Surukin Osama bin Laden kuma kakakinsa zai gurfana a gaban kotun Amurka bayan an cafke shi a kasar Jordan, inda zai fuskanci zargin hada baki wajen kai wa Amurkawa hari.
Wallafawa ranar:
Talla
An ce Sulaiman Abu Ghaith mai shekaru 47, dan asalin kasar Kuwait ne, kuma yana matsayin daya daga cikin masu Magana da yawun kungiyar Al-Qaeda.
Ana zargin shi da hade baki, da tsara yadda aka a hallaka Amurkawa kusan dubu uku, a harin ranar 11 ga watan Satuban shekarar 2001.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu