Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa da Amurka sun amince su gaggauta mika kasar Mali ga dakarun Afrika

Faransa da Amurka sun amince su gaggauta mika ragamar tafiyar da harakokin tsaron Mali zuwa ga Dakarun Afrika karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya. Bayan ganawa da Shugaban Faransa Francois Hollande a birnin Paris, mataimakin shugaban Amurka Joe Biden yace Gwamnatin Amurka ta jinjinawa Faransa a yakin da ta kaddamar a Mali.  

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande (Dama) da mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe biden (Hagu) a lokacin ziyarar da ya kai Paris
Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande (Dama) da mataimakin shugaban kasar Amurka, Joe biden (Hagu) a lokacin ziyarar da ya kai Paris REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

“Mun amince da bukatar gaggauta tura dakarun Afrika zuwa Mali domin tafiyar da harakokin tsaron kasar. Haka kuma muna masu goyon bayan jagorancin Faransa a Mali domin tabbatar da Demokradiya a kasar.” Inji Biden.

A ranar Lahadi ne Biden ya isa birnin Paris bayan halartar taro a birnin Munich dake kasar Jamus inda aka tattauna batutuwan tsaro a duniya, kuma a yau Talata ne ake san ran zai yada zango a London inda ake sa ran zai gana da Firaministan Birtaniya, David Cameron.

Akalla dakarun hadin gwiwa na Afrika, 8,000 ake shirin mika tsaron kasar ta Mali a hanunsu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.