Isa ga babban shafi
India

Mutane biyar da ake zargi da yin fyade da kisan kai a India sun ki amsa laifukan da ake tuhumarsu akai

Mutane biyar da ake zargi da yin fyade da kisan kai a kasar India sun ki amsa laifinsu a yau Asabar yayin da aka gurfanar da su a gaban kotu. A watan Dismbar bara ne a kawa wata dalibar kiwon lafiya fyade a cikin mota kirar bas, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta daga karshe, ya koma haddasa mummunan bore a kasar ta India.  

Motar Bas dauke da mutane biyar da ake zargi da yin fyda da kisa a yayin da aka gurfanar da su a gaban kotu
Motar Bas dauke da mutane biyar da ake zargi da yin fyda da kisa a yayin da aka gurfanar da su a gaban kotu REUTERS/Stringer
Talla

Ana tuhumar mutanen da laifukan fyade, kisa da kuma yin garkuwa wanda ake gudanar da shi a wata kotu dake birnin New Delhi.

“Dukkanin wadanda ake zargi da laifukan sun ki amsa laifinsu.” Inji v.k Anand, Lauyan da ya ke karesu.

Mutum na shida da ake tuhuma a shari’ar har ila yau an gurfanar da shi ne a gaban kotun masu kananan shekaru.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.