Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta ware Euro miliyan 1.2 don taimakawa ‘Yan tawayen Syria

Kasar Faransa ta ware kudaden da suka kai Euro miliyan daya da dubu dari biyu, a matsayi tallafin gaggawa, da za ta baiwa ‘Yan tawayen Syria, da suka kafa sabuwar Majalisar gudanarwar hadin gwiwa. Wannan matakin na Faransa na zuwa ne a daidai lokacin da ‘Yan tawayen suka yi wani taron neman goyon bayan kasashen duniya.  

Shugaban kasar Faransa, François Hollande
Shugaban kasar Faransa, François Hollande
Talla

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, da ya bayar da sanarwar tallafin ya ce, halin rayuwa na cigaba da tabarbarewa a kasar ta Syria, don haka dole kasashen duniya su kai dauki.
 

Ya ce Faransa, da ita ce ta fara amincewa da majalisar ‘Yan tawayen a matsayin mai wakiltar al’ummar Syria, na fatan ganin sun fidda ‘yan kasar daga mummunan halin da suke ciki.
 

A yau kuma ake sa ran Firaminsitan, kasar Rasha, Dmitri Medvedev, zai kai ziyara Faransa, inda zai tattauna da Shugaba Francois Hollande, kan batun kasar ta Syria.
 

Da ma Medvedev ya dade yana sukar matakan da hukumomin birnin Paris ke dauka na goyon bayan ‘Yan tawayen, inda ya ce hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa.
 

A farkon wannan watan aka kafa majalisar Gudanarwar ‘Yan tawayen na Syria, kuma zuwa yanzu Kasashen Yakin Gulf da suka hada da Saudi Arabia, Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabawa, Oman, Qatar da Kuwait sun amince da ita.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.