Isa ga babban shafi
Syria

Syria za ta yi amfani da makamai masu guba idan aka nemi a yi mata taron dangi

Gwamnatin Syria tace za ta yi amfani da muggan magamai masu guba idan har aka nemi a yi mata taron dangi. Amma Gwamnatin tace za ta kauracewa amfani da makaman ga ‘Yan tawayen kasar masu kokarin kawo karshen mulkin Bashar Assad.

Shugaba Bashar al-Assad na Syria
Shugaba Bashar al-Assad na Syria Reuters/Sana/Handout
Talla

Wannan ne dai karo farko da Gwamnatin Syria ta fito ta amsa mallakar makamai masu guba, tana mai cewa za ta yi amfani da su idan kasashen Turai suka nemi yin katsalandan ga harakokinta.

Yanzu haka kuma wasu kasashen Turai da Isra’ila sun bayyana fargaba game da yaduwar makamai ga sauran ‘Yan tawaye a duniya.

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama, ya gargadi shugaban Syria Bashar al Assad, domin kaucewa amfani da makaman masu guba ga ‘Yan Tawayen kasar.

Obama ya shaidawa taron tsoffin sojin kasar cewa, duniya na kallon shugaba Assad da mukarrabansa, domin kaucewa amfani da muggan makaman ga al’ummar Syria.

Ministan harkokin wajen Syria, Jihad Makdissi, yace za su yi amfani da makaman ne domin kare kansu daga hare haren da wasu kasashe ke shirin kaddamarwa a Syria

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.