Isa ga babban shafi
Rasha-China

Putin na Rasha ya fara ziyara a China

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya fara ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar China, inda ake sa ran kasashen biyu zasu tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da huldar makamashi da rikicin Syria da batun Nukiliyar Iran. A yau Talata ne Putin zai gana da Hu jintao Shugaban China.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin tare da takwaransa na China Hu Jintao.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin tare da takwaransa na China Hu Jintao.
Talla

Bayanai na cewa, shugaba Putin zai gana da shugabanin kasashen Iran da Afghanistan a asirce.

Wannan ce ziyarar Putin ta Farko a China tun sake zaben shi karo na uku a matsayin shugaban Rasha.

Putin da Hu suna cikin shugabannin da zasu halarci taron kasashe Shida a Shanghai, wadanda ke neman iganta huldar kasuwanci domin watsi da bukatun kasashen Yammaci.

An dade dai kasar Rasha da China suna hawa kujerar Na-ki game da rikicin Syria a zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Kazalika, kasashen sun dade suna adawa da matakin kakubawa kasar Iran Takunkumi akan shirinta na mallakar makaman Nukiliya.

Sai dai duk da wannan hadin kan kasashe akwai baraka tsakanin Rasha da China da suke neman dinkewa akan batun farashin Man Fetir a kasuwar Duniya.

Ziyarar Putin zuwa China ta biyo bayan kammala Taron kasashen Turai a St. Petersburg da Rasha ta dauki nauyi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.