Facebook ya fara sayar da Hannayen Jarinsa
Shafin Facebook na zumunta a Internet ya fara sayar da hannun jarinsa ga al’umma a yau Juma'a a kan kudi Dala Talatin da Takwas ($38) a ko wane hannun jari inda darajar Kamfanin ta kai Dala Biliyan Dari da Hudu $104.
Wallafawa ranar:
Shekaru Takwas ke nan da aka samar da Kamfanin Facebook a Intanet amma Kamfanin ya kafa tarihi a Amurka bayan kasacewa cikin manyan kamfanoni uku masu kima a kasar.
Kamfanin Facebook yanzu haka zai sayar da hannayen Jari Miliyan 180, inda inda darajar Kamfanin ta sha gaban Kamfanin Amazon da Cisco da kuma Kamfanin kera Mota na Ford.
Akwai sama da mutane Miliyan 900 masu amfani da Shafin Zumunta na Facebook a Duniya cikin shekaru Takwas da kafa kamfanin.
Masana tattalin arziki sun ce Hannayen Jarin Facebook zasu tashi sama duk da yawan hannayen da aka sa a kasuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu