Isa ga babban shafi
Syria-MDD-Turkiya

Dubban masu adawa da Assad sun tarbi Annan a sassanin ‘Yan gudun hijira

Daruruwan ‘Yan gudun hijirar kasar Syria sun tarbi ziyarar babban mai shiga tsakani rikicin kasar Kofi Annan, a sansaninsu da ke kan iyaka da kasar Turkiya, tare da shewar kyamatar shugaba Bashar al-Assad.

Ziyarar Kofi Annan a sansanin 'Yan gudun Hijira a kasar Turkiya inda wassu yara ke masa maraba a lokacin ziyarar shi
Ziyarar Kofi Annan a sansanin 'Yan gudun Hijira a kasar Turkiya inda wassu yara ke masa maraba a lokacin ziyarar shi REUTERS/Umit Bektas
Talla

Annan ya kai ziyarar ne a dai dai lokacin da wa’adin da aka dibar wa gwamantin Assad na janye dakarun shi daga yankunan ‘Yan adawa ya kawo karshe.

Gwamnatin Turkiya ce ta ginawa ‘Yan kasar Syria sansanni a Yayladagi, Kuma Kofi Annan ya samu tarba daga ‘Yan gudun hijirar wadanda ke dauke da tutar kasar Syria da Tutar kasar Turkiya.

Bayan kai ziyarar, Mista Annan ya shaidawa manema Labarai har yanzu dakarun Bashar Assad suna kai hare hare a wasu yankunan ‘Yan adawa bayan tabbacin da gwamnatin taba shi na tsagaita wuta.

Annan yace tsarin sasanta rikicin Syria yana kan bisa hanya.

Sai dai a wani sako da mista Annan ya aikawa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin yace babu wani alamu da Gwamnatin Syria ta nuna na tsagaita wuta.

Mutane kimanin 25,000 ne suka yi gudun hijira daga Syria zuwa kasar Turkiya. Fira Ministan Turkiya Tayyip Erdogan yace sun kashe kudade Dala miliyan 150 saboda kula da hidimar ‘Yan gudun Hijira.

Majalisar Dinkin Duniya tace sama da mutane 9,000 ne suka mutu tun fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar al Assad a bara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.