Isa ga babban shafi
Indiya

Taron Shugabannin kasashen dake samun bunkasan tattalin arziki

Manyan kasashen duniya masu tasowa ta fannin tattalin arziki guda biyar, a wajen taronsu na yau Alhamis a birnin Delhi a kasar Indiya, sun cimma matsaya cewa, hanyar tattaaunawa kawai ce, zata iya magance matsalar zubar da jinin da ake yi a kasar Syria, da kuma ja in ja kan shirin nukliyar kasar Iran.

REUTERS/Yekaterina Shtukina/RIA Novosti/Kremlin
Talla

Shuwagabannin kasashen Brazil, Rasha, Indiya, China da kuma kasar Afrika ta kudu, bayan amincewa da wanan hanya sabanin yin amfani da karfin soja, da wasu kasashen yammaci ke ikrarin, har ila yau sun cimma wata matsaya, ta samar da katafaren bankin ci gaba kishiya ga hukumomin kudin ksashen yammaci.

A lokacin da yake bada sanarwar bayan taron kasashen karo na 4 a birnin Delhi, Fira Ministan Indiya Manmohan Singh ya ce, ba tare da wata ja-in ja ba kasashen nasu sun cimma matsaya kan fifita hanyar tattaunawa, wajen magance matsalolin wadannan kasashen Iran da Syriya fiye da yin amfani da karfi.

Su dai manyan kasashen biyar masu tasowa da ake kira gamayar kasashen Brics, wadanda ke da 40% na yawan al’umar duniya, na ci gaba da kokarin neman bunkasa tattalin arzikinsu ne ta yadda zai yi tasiri a duniya, duk kuwa da banbace banbance muradu dake a tsakaninsu.

Shugaban kasar Rasha Dimtri Medvedev, ya shaidawa manema labarai cewa, nan gaba gungun kasashen guda 5 na da niya mayar da kungiyar tasu mai karfin fada a ji a duniya, a ya yin da a nasa bangaren shugaban kasar Chana Hu Jintao ya ce, ya samun banbance banbancen dake tsakaninsu wata dama ce ta yin amfani da karfn ko wace kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.