Isa ga babban shafi
Amnesty

Kungiyar Amnesty ta nuna damuwa kan karuwar aiwatar da hukuncin kisa

Kungiyar Amnesty International, ta bayyana damuwar ta kan karuwar aiwatar da kisan kai a duniya, inda take cewa a bara kawai, an kashe 656.Rahotan kungiyar da ta fitar yau Talata, ya nuna cewar akalla mutane 676 aka aiwatar wa da kisan kan a shekarar da ta gabata, a kasashe 20, wanda hakan ya nuna karuwar yawan wadanda ake kashewa.

Talla

Rahotan ya bayyana kasashen Iraqi, Iran da Saudiya, a matsayin kasashen da aka fi aiwatar da kisan,

Kungiyar ta ce, a kasar Iraqi an kashe mutane 360 a Iran, 82 a Saudi Arabia, 68 a Iraqi, 43 a Amurka, yayin da China kuwa ba a ma labari, saboda sun zarce 1,000.

Rahotan ya kara da cewa, an aiwatar da kisan kai ga mutane 41 a Yemen, 30 a Koriya ta Arewa, da kuma 10 a Somaliya.

Sakatare Janar na kungiyar, Salil Shetty, ya ce yanzu ta tababta cewar, kasashe 178 na duniya, sun daina aiwatar da kisan kai, wanda hakan ba karamar c igaba bane a duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.