Isa ga babban shafi
Durban

An cim ma Matsaya don magance dumamar yanayi a taron Durban

Bayan shafe kwanaki 14 suna tafka muhawara a birnin Durban na kasar Africa ta kudu, wakilan kasashen da ke halaratar taron yaki da dumamar yanayi sun cim ma matsaya kan yadda zasu shawo kan lamarin.

Wakilan kasashen Duniya a zauren Taron Dumamar yanayi a birnin Durban kasar Africa ta kudu
Wakilan kasashen Duniya a zauren Taron Dumamar yanayi a birnin Durban kasar Africa ta kudu REUTERS/Rogan Ward
Talla

Wakilan sun amince da taswirar da za ta kunshi dukkan kasashe nan da shekarar 2015, inda matakin zai fara aiki a shekarar 2020.

Shugabar kula da muhalli ta Majalisar Dunkin Duniya Christiana Figue tace bata yi tsammanin za a sami cim ma wata yarjejeniya ba, kuma yarjejeniyar da aka kula, ta nuna yadda wakilan ke karrama Nelson Mandela.

Kasashen Turai sun amince da yarjejeniyar, inda suka bayyana yarjeniyoyin da za a kulla nan gaba, da cewa za su yi karfin gaske, da kuma dole kasashe su amince da su.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya yi jinjina ga mahalarta taron. Ya kuma ce Nahiyar Africa ta yi rawar gani a wannan karon.

Kasashen India da China sun fara fitar da iska mai guba fiye da kima, a shekaru goma da suka gabata amma yarjejeniyar Kyoto ba ta yi aiki a kansu ba.

Yayin da amurka wadda ke a matsayi na 2 a kasashen da ke fitar da gurbataccen iska, ta ki sa hannu a kai a wancan lokacin don haka dokar bata hau kan ta ba. Amma da alama wannan karon dokar za ta yi aiki ga baki dayan kasashen.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.